Bayan sa hannu a wannan yarjejeniya sai Imam Hasan (a.s.) ya zauna a Kufa na wasu ‘yan kwanaki kadan, cikin kunan rai kan abin da ya faru, daga nan kuma sai ya yi haramar tafiya birnin kakansa Manzon Allah (s.a.w.a). Lokacin da ayarinsa ya yunkura, sai duk mutanen Kufa suka fito suna kukan kufcewar rabonsu, takaici na bayyana daga fuskokinsu; daga cikinsu daga mai kuka sai mai cizon yatsa saboda takaicin abin da ya faru. Yaya fa ba haka ba, alhali kuwa suna ganin kaskanci ya yi wa garinsu tabaibayi; ga askarawan Mu’awiya nan na yi wa Kufa tsinke, suna tsananta kamu gare shi (garin), suna haifar da tashin hankulan mutane, suna tafka kowane irin ta’addanci irin wanda ba a taba ganin irinsa ba; duk wanda ya bayar da kai bori ya hau ya zama munafuki zai sami kyautuka; wanda kuwa ya nuna hamayya za a kashe shi da mafi munin kisa.
Sai ayarin Imam Hasan (a.s.) ya bi sahara, yana mai shiga Madina. Mutanen Madina dai sun fito suka yo cincirindo don tarbar Imam da sauran Ahlulbaiti (a.s.), alhali albishir na bayyana daga fuskokinsu. Yaya fa ba haka ba, alhali kuwa albarka ta shigo musu, alhairai –da dukkan nau’o’insu- na fuskantar gidajensu.
Yana daidaita a gidansa sai Imam Hasan (a.s.) ya shiga aiwatar da aikinsa na isar da sako ta wani sabon salo. Idan har a jiya ya kasance shugaba da ke gudanar da al’amurran al’umma, yake kuma tsara matsa tsare-tsaren da za ta ginu a kai don gobenta, ta hanyar matsayin Immanci na bangare siyasa; to a yau, bayan yarjejeniyar sulhu, ya tsara wani sabon tafarki ne, yayin da ya tsara wani wani sabon tafarki, ya kirkiri wata makaranta ta tunani mai girma da yake shugabancinta, don ta zama cibiyar yaduwar shiriya da tunanin Musulunci. Hakika kuwa kwalliyar wannan makaranta ta Imam (a.s.) ta biya kudin sabulu har ta nunka sau biyu, yayin da ta yaye hamshakan malamai da manyan masu ruyawa.
Tare da cewa wadannan ayyukan Musulunci na Imam Hasan (a.s.) ba su boyu ba ga mahukuntan Umay-yawa, don haka mahukuntan suka kasance cikin hasashen matsayin ayyukan da sakamakonsu a nan gaba; don haka sai Umayyawan suka kuduri aniyar bin matakin siyasa don gamawa da Imam da shugabancinsa na Musulunci. Manyan rukunnan da wannan siyasa ta ginu a kai su ne:
1- Koran shugabannin Muminai a dukkan garuruwan Musulmi, da kashe da yawa daga cikinsu, irin su Hijir bin Udai da mutanensa, da su Rashidu al-Hijri, Amr bin al-Humk al-Khuza’i da dai sauransu.
2- Kuntatawa duk ‘yan Shi’ar Ali (a.s.) da wulakanci, tozarci, kora, toshe hanyoyin abinci, ta’addanci, rushe gidaje da matsugunnai da sauran irin su.
A kan haka Mu’awiya ya yi amfani da miyagun gwamnoninsa da wasu karkatattun mutane irin su Mugirah bin Shu’ubah, Samrata bin Jundubi da Ziyad bin Abihi (wanda ba a san babansa na hakika ba), wanda ya nada gwamna a Iraki. Ziyad ya kasance dan zina ne, sai Mu’awiya ya yi masa sutura ya sadar da shi da baban shi (Abu Sufyan) ya mayar da shi dan’uwansa. Littafan tarihi sun hakaito laifukan Ziyad da cewa:
“Ziyad ya rika bin ‘yan Shi’ar Ali bin Abi Dalib yana kashe su ko ina har sai da ya kashe talikai masu yawa daga cikin su. Ya shiga yanke hannuwansu da kafafunsu, yana tsire idanuwansu. Ya zama yana rudin Mu’awiya da –samun kusanci da shi- da kashe su ([1])”.
3- Neman agajin wasu malaman fada wajen yiwa rayuwar Ahlulbaiti (a.s.), musamman Imam Hasan (a.s.), bakin fenti. Mu’awiya ya sa zagin Imam Ali (a.s.) ya zama al’ada a kan mumbarorin da cikin hudubobin sallar juma’a. Ta wani gefe kuma ga wasu hadisai (na kayra) masu rufa masa da kunigiyarsa. Ya kirkiri lalatattun akidu ya dangana su ga Shi’a, mabiya Ahlulbaiti (a.s.), da nufin bata surarsu a kwakwalen mutane.
4- Watsa dukiya babu kakkautawa ga shugabannin kabilu da yake tsoron hamayyarsu.
5- Karshen tsarin wannan muguwar siyasa shi ne kashe Imam Hasan (a.s.) da guba, yayin da Mu’awiya ya shayar da shi guba ta hanyar matarsa (Imam din) mai suna Ja’adatu bin Ash’ath.
Haka Imam Hasan (a.s.) ya bar duniya zuwa ga Ubangijnsa a lokacin yana wani fage daga fagagen jihadi saboda sakon Musulunci wanda kakansa Manzon Allah (s.a.w.a) ke jagoranci. Shahadarsa ta kasance a ranar 7 ga watan Safar na shekarar hijira ta hamsin.
Tun kafin shahadarsa dai, Imam Hasan (a.s.) ya yi wasici da a bisne shi a kusa da kakansa Manzon Allah (s.a.w.a). Sai dai Umayyawa, karkashin Marwan bin Hakam, sun hana aiwatar da hakan, yayin da suka dage wajen ganin sai sun raba tsakanin Manzon Allah (s.a.w.a) da jikansa, dan gaban-goshinsa kuma masoyinsa Hasan, shugaban samarin gidan Aljanna. Wannan ya sa dole Ahlulbaiti (a.s.) suka tafi suka bisne shi a Makabartar Baki’a.
Amincin Allah ya tabbata a gare ka Ya Aba Muhammad, wanda aka zalunta a rayuwarka da bayan shahadarka, ranar da aka haifeka, ranar da ka yi shahada da kuma ranar da za a tayar da kai alhali kana rayayye.
________
([1]).Al-Futuh na A’atham al-Kufi juzu’i na 4, shafi na 161.